Ƙaramin Yaro ya tsaida Zirga Zirgan Ababen Hawa cak yayin gudanar da Sallaarsa akan titi.
Wani yaro musulmi ya tada kura a kan hanya, yayin daya shimfida dadduma ya dinga yin sallah abin sa ba tare daya girgiza ko yin gizau ba abinsa.
A wani gajeren bidiyo da aka wallafa a kafar sadarwa ta Tiktok, an hango yaron yana sunkuyawa tare da mikewa, hadi da yin ruku’u da sujjada kamar dai yadda duk wani musulmi yake yi yayin da yake gabatar da sallar sa.
Tuni dai wannan Bidiyon da aka wallafa yaja hankalin masu kallo wanda tuni aka kalle shi kimanin adadi miliyan 6.
Duk da wannan rashin tsoro da yaron ya nuna hade da jarumta, sai da wani jami’in tsaro yaso ya kawar dashi daga kan titi amma hakan ta gagara.
Koda jami’in tsaron yaga haka, sai ya tsaya kusa dashi, ya ci gaba da bashi kariya, tare da bawa ababen hawa hannu a kokarin da suke na wucewa.
Masu wucewa haka suka dinga rabewa suna wucewa, yayin da suka cika da mamakin kallon yaron daya maida hankali cikin natsuwa yana bautawa ubangiji madaukakin sarki.
Yadda mutane suka bayyana ra’ayin su bayan sun kalla:
“Hakan ba daidai bane, don Allah ku koya masa yayi abinda ya dace domin maida duniyar wuri mai cike da zaman lafiya”.
@eshunkwabena sai yace:
“Hakan ba daidai bane gaskiya. Ubangiji bazai amshi lamarin bautar nan ba, aikin riya ne ke sawa koda yaushe mutane ke irin wannan bautar. Muyi amfani da kwakwalwar mu ta mutane muyi bauta”.
“Nan gaba yayi ta a tsakiyar babban hanya inya isa, da an kalle ka yadda ya dace”.
“Ban san waye ya raini wannan yaron kamar dan Afurka ba”.
Quamjan ya fusata yace: Wannan daukewar hankali ne! Akan me za a yi ibada akan titi tsakiya? Akan ne?
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.