Dalilan da ya sa lauyoyin ke neman haƙƙoƙin Alh. Hamisu Bala wadume shi ne, wanda Abba Kyari ya kwashe masa motoci da sauran kayayyakinsa na more rayuwa, bayan kamasa da shi Abba kyarin yayi bisa zargi na satar mutane da aka ce Wadume yayi, saɓanin biyo bayan rahotonni suke tabbatar da cewa lallai Wadume ba zai taɓa aikata wannan ta’asarba domin yarface kawai irin ta Siyasa.”
Abba Kyari ya kwashe motocinsa goma sha biyar! Wanda ya haɗa da Motoci ƙirar Sharon guda shida, Golf 3, GLK Mercedes Benz guda ɗaya, J5 mai buɗewa guda biyu, babban mota ƙurar tirela guda biyu 911, sai kuma bas din homa guda biyu, da Toyota Corolla LE ɗaya, suna yin motoci goma sha biyar.
Tsohon DSP Abba Kyari ya kwashe jakunkuna masu yawa na egusi na Alh Hamisu Bala wadume, Abba da yaransa sun karɓi kuɗi a hannun yaran wadume, bayan da shi Kyari ya tilasta musu sayar da shanun Wadume.
Jami’in tsaron wato Abba kyari Sun ɓata sunansa a duk duniya! Abba da yaransa sun ɓata sunan mutumin kirki Alh. Hamisu Wadume ɗan asalin garin Ibi jihar Taraba, a tsawon shekaru uku Wadume na tsare da shari’a, babu wanda ya zo ya tuhume shi da sace mutane ko zamba. An kama shi a Kano ba tare da wani makami a hannunsa ba, ta yaya a duniya zai zama mai garkuwa da mutane, ko dan fashi ko dan ta’adda?
Kamar yadda rahotonni suka bayyana daga dubbannin al’umma cewa, Wadume mutum ne, wanda kullum yake cuɗanya da jama’ar gari, ba ya barin garinsa wato Ibi jihar Taraba tsawon mako guda, yana taimakon kowa da kowa ba tare da la’akari da imani ba, duk wannan ya faru ne saboda ra’ayi daban-daban na siyasa (jam’iyya) , ba wani abu ba face wannan.
Al’ummar garinsa shi Alh. Hamisu Wadume a kullum suna addu’a sosai cewa idan abin da Abba Kyari ya yi shi ne abin da ya kamata a yi adalci ya yi nasara, amma idan ba haka ba, to ya girbi abin da ya shuka, ba shakka acigaba da cewar al’ummar garin na Ibi Addu’ar su ya amsu duba ga yadda Abba kyari shima ya faɗa tsaka mai wuya a dalilin tabbatar da Safarar miyagun ƙwayoyi.
Tun farko wadume ya tsallake rijiya da baya, wasu da ba’a san ko su waye ba ne suka yi garkuwa da shi, masu son sa sun bi motar har sojoji suka shiga tsakani, ta yaya zai zama dan ta’adda? Kuma waɗancan gidajen yada labarai da suka cigaba da kiran sa da yin garkuwa da sarki koda bayan yanke hukunci, za mu haɗu a kotu.
Saboda waɗannan dalilai, muna neman gyara da kayansa. A bar Abba Kyari ya dawo da kadarorinsa duk a cewar al’umma masu inkari da cewa Wadume ɗan ta’addane, duk motocin da aka ambata bayanansu, direbobin da aka kama motocin a hannunsu suna nan, Babu direban da ya rasu, Kuma a shirye suke su ba da shaida a gaban kotu na huɗu dake birnin Tarayya Abuja “Court 4”.