Ƙungiyar ICPC ta sake kama tsohon magatakardar JAMB.
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifukan da ke da alaka da cin hanci da rashawa (ICPC) ta sake kama tsohon magatakardar Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB), Farfesa Adedibu Ojerinde a ranar Alhamis a Abuja.
Sake kama Farfesa Ojerinde ya biyo bayan sammacin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar.
Ana sa ran zai fuskanci tawagar masu bincike kan sabbin shaidun da aka gano dangane da shari’ar da ake yi na karkatar da kudade a lokacin da yake jami’in gwamnati.
Jami’an ICPC sun bankado wasu asusu guda biyu da aka bude a cikin sunayen Trillium Learning Center Ltd da Sapati International Schools Ltd inda aka karkatar da kudaden ta hanyar amfani da sunayen dalibai na bogi.
A ranar 12 ga watan Disamba, 2022 Hukumar ta gayyaci tsohon magatakardar JAMB domin amsa tambayoyi kan sabbin shaidun amma ya rubuta ta hannun lauyansa yana neman alfarmar kwanaki 14 don ba shi damar girmama gayyatar. Ojerinde, ya ki amsa gayyatar kamar yadda lauyansa ya yi bayan cikar wa’adin kwanaki 14 a ranar 27 ga Disamba, 2022.
A ci gaba da binciken da hukumar ta gudanar, hukumar ta gano wasu sabbin shaidu da ke nuna cewa Ojerinde ne kadai ya sanya hannu kan asusun ajiyar banki daban-daban da ake gudanarwa da sunan Trillium Learning Center Ltd da Sapati International School Ltd.
Takardu a sunayen Joshua Olakulehin Olaniran da Akanbi Lamidi. Ya kuma yi amfani da wani shaidar karya, Adeniyi Banji wajen gudanar da wani asusu na daban da sunan Standout Institutes Ltd.
Rahoto: Shamsu S Abbakar Mairiga.