Daga Rafi’atu Mustapha Katsina.
Wasu Maharan Bazata Wadanda Su Kayi Garkuwa Da Caliban Jami’a na Najeriya Wadanda Su kayi Tafiya Zuwa Nsukka Kusa Da Babbar Hanyar Ugwuogo-Nike, A Ranar Lahadi.
An Bukaci Farashin Naira Milyan 300, Ba a Gama Tantance Ko Dalibai Nawa Sukayi Garkuwa Da Suba Amma Wani Kiyascin Ya Nuna Su 10 ne.
Wani Dan’uwan Daya Daga Cikin Daliban Da akayi Garkuwan Dashi Ya Bayyana ma Manema Labarai Hakan A Yammacin Ranar Laraba, Cewa Wadanda Akayi Garkuwan Dasu Hada Dan’uwansa, Kuma Sun Nemi Farashin Naira Milyan 300 Domin Su Sakesu.
Kamar Yadda Yace Masu Garkuwan Su Bakwai Ne Kuma Duk Fulanine, Yace Masu Garkuwan Sun Dakatar Da Basu Naira 500,000 Da akayi A Matsayin Farashin Da Zasu Sakesu.
A Yanzu Suna Ikirarin Zasu Kashe Su Idan Ba a Kawo Musu Cikakkun Kudin Ba.