Wasu ƴan Bindiga guda 3 sun shiga cikin Haramin ƙannen Al- Ridha wato Sheikh Ahmad da ɗan uwan sa Sheikh Muhammad da suke kwance a garin Shiraz Iran Harami mafi girma na 3 a ƙasar, sun kashe Maziyarta haramin 13 cikin su harda Mata da Yara guda.”
Shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi, ya ce harin Haramin Shah Cheragh, na ta’addancin maƙiya baze sake faruwa ba, tuni aka kama mutum 2 cikin su maharan. Yana mai cewa jami’an tsaron kasar za su koyar da darasi ga wadanda suka tsara harin ta’addancin. A wani labarin kuma jagoran juyin juhali na ƙasar Iran ɗin Ali Khamene’i yayi addu’ar ga waɗanda aka kashe tare da Iyalan su.