Rundunar ƴan sandan jihar Ogun ta cafke budurwa ƴar shekara 29 mai suna “Chioma Okafor” da “Nweke Joshua” ɗan shekara 19 a yayin da suke gudanar da wani samame na fashi da bindigar roba a unguwar Adesan da ke Mowe.
Kakakin rundunar ƴan sandan, Abimbola Oyeyemi, a ranar Lahadi, a Abeokuta, ya shaida wa manema labarai cewa, an kama waɗanda ake zargin ne biyo bayan wata waya da suka samu a hedikwatar Mowe.
Ya ce an sanar da ƴan sanda cewa wasu ƴan fashi da makami sun kai farmaki wani kantin sayar da kayan abinci mallakar wani “Johnson Nwokoro” da ke Safari Junction Adesan tare da korar mai sayar da ranar.
Oyeyemi ya ce bayan an kai musu ɗaukin gaggawa ne DPO na sashen Mowe, SP Folake Afeniforo, ya yi gaggawar tara tawagar ƴan sintiri na sashin da ƴan ƙungiyar So-Safe zuwa wajen da aka cafke mutanen biyu.
Ya ce “A binciken su, an gano cewa sun zo ne domin su yi wa shagon fashi da bindigogin wasan yara masu kama da na asali.
“Da ake yi masa tambayoyi, ɗan shekara 19, Nweke Joshua, ya shaida wa ƴan sanda cewa, Chioma Okafor ce ta zo da tunanin aiwatar da aikin fashin domin su samu wasu kuɗaɗe.
“Ya kara da cewa Chioma ce ta sayi bindigogin wasan yara guda biyu ta kuma ba shi guda daya da zai yi amfani da shi wajen aikin.
“Sun je shagon ne suka yi kamar su kwastomomi ne, amma kwatsam sai suka fito da bindigogi suka umarci mai shagon ya miƙa musu duk kuɗin da yake hannunsa. Sa’a ya kure musu lokacin da ƴaan sanda da jami’an tsaro suka isa wurin kafin su tsere.”
Oyeyemi ya ce kwamishinan ƴan sanda, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin a miƙa waɗanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da bincike mai zurfi.
Rahoto Shamsu S Abubakar Mairiga.