Jami’an ‘yan sandan Najeriya sun zargi manyan hukumomi da yin sama da faɗi da kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ta yarda Da’u fitar domin a baiwa Ƴan Sandar Nijeriya na wata bakwai, bisani Sai manyan hukumomin Ƴan Sandan suka bada na wata ɗai-ɗai.”
A cewarsu, gwamnatin Najeriya a shekarar da ta gabata ta amince da ɗaya daga cikin buƙatun Ƴan sandar ta hanyar amincewa da karin albashi ga jami’an ‘yan sanda daga watan Janairun 2022.
Sun bayyana cewa ƙarin ya fara aiki ne a watan Yulin shekarar 2022 inda aka aika da saƙon ga kowane jami’i domin sanar da jami’an yadda za a biya kuɗaɗen. A cewarsa, ana bin su bashin sabon kunshin albashin na watan Janairu har zuwa watan Yuni.
Da yake magana da Alfijir Hausa ɗaya daga cikin ‘yan sandan da suka fusata ya ce ya kamata a biya su bashin watanni shida, yana mai jaddada cewa har yau ba a biya kuɗin ba.”
Ya ce, “Hukumar ‘yan sanda na shirin wawure haƙƙin ƙananan mukamai da gwamnatin tarayyar Najeriya ta ba da a basu.”
“Ba’a aiwatar da wannan ƙarin ba sai watan Yuli da aka aika da saƙon ga kowane jami’in da zai ba da lacca kan yadda za’a biya kudaden.”
“A cikin saƙon na ƙananan Ƴan sandar sun ce za’a ba su bambanci na wata ɗaya tsakanin tsohon da sabon tsarin albashi kamar yadda suka saba.
“A ranar 12 ga wannan watan (Yuli), an biya ‘yan sanda Naira 32,930, an biya wa ‘yan sanda kusan Naira 35,000 ga Sajan, kusan Naira 42,000 ga Sajan, sannan an biya sufetoci kusan N85,000.
“Lokacin da watan ya ƙare, rabin waɗannan kudaden ne kawai aka ƙara mana albashi daban-daban amma muka yi shiru saboda mun riga mun shiga tarkon dokokin ƙungiyar.”
“Saboda da haka za’a fara aiki daga watan Janairu, ya kamata a biya mu bashin watanni shida (watau dan sanda ya kamata a biya 32,930 × 6 wanda ya kai jimlar N197,580, haka kuma ga Kofur, Saje da Inspectors) amma har yau, wannan kudi ba’a biya ba.”
“Kowa ya yi shiru kamar ba abin da ya faru, don Allah a sanar da duniya dalilin rashin tsaro a Najeriya, ba za su iya zama a ofisoshinsu masu kyau ba su ci gaba da wawure mana hakkokinmu alhali muna can cikin daji muna neman mutuwa ba tare da mun sani ba. abin da iyalanmu za su ci washegari,” wata majiya ta kara da cewa.”