Daga Shamsu S Abbakar Mairiga.
“Olorunsogo Bamidele” ƴar sanda daga jihar Ogun, ma’aikaciya daga shelkwatar ƴan sanda ta “Ode Omu” tayi suka kan yanda nasama da ita a gun aiki mai suna “DCO ASP Ajayi Matthew” yaso yayi lalata da ita. dama wasu halayya marasa kyau da ya ke yin mata.
Kamar yan da ta bayyana a faifan bidiyo, “Olorunsogo Bamidele” ta kalubalanci “ASP Ajayi Matthew” Kan yan da yake nuna sha’awar sa a kan ta, ta hanyan amfani da matsayin sa na son Kwanciya da wanda yafi su matsayi a gun aiki.
Ƴar sandar tace, “yana tafiyar da mune, ta yanda yakan ce inmuka fada mawani, to sai ya kore mu a gun aiki. Muddab mace taki basa haɗin kai sai yace zai koreta daga gun aiki”
Yar sandar wanda wanda jikin ta ya bayyana da tabbai a cikin faifan bidiyo, tana mai cike da kuka, kana cike da neman taimako a kan yanda mai gidan nata ya mata dukan tsiya. saboda kin amincewa yayi lalata da ita. sannan yayi mata zindir haihuwar uwa, a gaban ƴan uwan aikin ta da kuma wanda ba ma’aikata bane.
Yanda tace, tasamu nasaran tserewa ne, da taimakon wanda laifi ne takawo su shelkwatar ƴan sandar ta su.