A shekaran jiya ne ɓarayin dajin dake yankunan Ɗan-musa jihar Katsina suka ɗauki aniyar yin mauludi.
Rahoton na cigaba da cewa, Amma sai dai wani shugaban Daba wanda ake kira da Oga hizga ya kafe yace bai yarda suyi wannan mauludi ba harsai sun saya masa sabon mashin.
To amma kuma su ɓarayin da suke son shirya mauludin sun kafe cewa, baza su sayawa shi ɗan Daban mashin ɗin ba, daga nan ne dai tarzoma ta tashi tsakanin shi da yaran shi da kuma masu son shirya mauludin wato ɓarayin.”
ALFIJIR HAUSA ta bibiyi lamarin inda ta ƙara samun wani labari na ɓallewar rikici tsakanin Ƴan fashin dajin da shi tawagar hizga, Ƴan fashin dajin sun samu nasarar kashe Oga hizga ɗin da kuma kashe wayansu yaran shi guda huɗu, Amma kuma shedun gani da ido sun shaidawa ALFIJIR HAUSA cewa daga cikin yaran nashi huɗu da aka kashe biyu daga cikin su Abzinawa ne.”
Shidai Oga hizga din shineɓbarawon daya addabi yankunan Ɗan-musa, turare, da Ƴantumaki wani lokacin ya kanzo da dakarunsa wani lokacin kuma yakanyo gayya daga Zamfara.”
Rahoto: Zaharaddeen Sani Dutsin-ma.