Ɓarayin Haure Ke Haifar Da Ƙarancin Man Fetur A Najeriya – Gwamnatin Tarayya ta bayyanawa ƴan Nijeriya.
Gwamnatin tarayya ta dora alhakin matsalar karancin man fetur da ake fama da shi a kasar baki daya kan barayin haure
Ta kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa kasar na da wadataccen man fetur sama da lita biliyan 1.6.
Majiyar Alfijir Hausa ta ruwaito hakan a cikin wata sanarwa da hukumar sa ido kan harkokin man fetur ta Najeriya Midstream and Downstream, ta hannun Sashen Sadarwa na Kamfanin NMDPRA ta fitar ranar Juma’a.
Domin warware matsalar karancin man fetur da ake fama da shi yanzu haka, Hukumar ta ce za ta yi amfani da gyare-gyare mai sauki a farashin jigilar kayayyaki domin magance illar da farashin ke ci gaba da gamuwa da tazgaro a wajen masu jigilarsa.
Ta kara da cewa, za ta tabbatar da sarrafa kayayyakin da ake sayar da su musamman na bukata, da samar da tsarin sa ido tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro na gwamnati don tsawaita sa’o’in aiki a wuraren lodi da ma’ajiyar kaya da kuma wasu zababbun tashoshi masu cike da kaya.