Daga Shamsu A Abubakar Mairiga.
Yanda ɗan sanda ya caka ma ɗan uwansa ɗan sanda alkamashi a jihar Kebbi.
Jami’an rundunar ƴan sandar jihar Kebbi, ta sanar da cewa jami’inta mai suna “ASP Abdullahi Garba” ya kashe ɗan uwansa “ASP Shu’aibu Sani Malumfashi” ta hanyar caka mai alkamashi.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandar jihar Kebbin “SP Nafi’u Abubakar” ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Jami’in hulɗa da jama’a ya tabbatar da hakan, inda yace “Abdullahi Garba ya kashe “Malumfashi” ne ta hanyar caka masa alkamashi bayan wani ɗan hatsaniya da suka samu. bayan kuma ansaba ganin su tare a cikin ƙaramar hukumar ta Argungun ta cikin jihar Kebbi a wajan aikin su”
Nan-da-nan aka garzaya da “Malumfashi” asibin Birnin Kebbi inda likitoci suka tabbatar da mutuwar sa.
Marigayin dai tsohon jam’i’in binciken laifuffuka ne na 11, a cikin shelkwata ta jihar Kebbi kafin mutuwar sa.
“SP Nafi’u Abubakar” yace ammiƙa mai laifin ga jami’an bincike domin cigaba da bincike.