Murnar zagayowar ranar haihuwar ɗan takaran shugaban kasar Nijeriya ƙarƙashin Jam’iyar PDP, Alh. Atiku Abubakar yayin da ya cika shekaru 76 a duniya a yau Juma’a, bisani Nasarorin da ya samu wajen cigaban al’ummar mu ba abin mantawa ba ne, duba ga yadda Ɗan takaran ya kafa wasu cibiyoyin da al’umma za su dogara da kan su.”
Ya duƙufa wajen laluɓo hanyoyin magance matsalolin da ke cigaba da addabar kasarmu, hatta takararsa ya fi domin ceto Najeriya.
‘Yan Najeriya suna alfahari da irin sadaukarwar da ya yi wa kasa Nijeriya, da hakane Ƴan Nijeriya ke cewa Atiku Abubakar shugaba ne na gaskiya.”
“Alh. Atiku Abubakar, ya matuƙar taka rawar gani a rayuwar matasan Nijeriya, duba ga yadda ba shi da wani manufa face ganin matasa sun dogara da kan su.”
A dalili hakane ɗan takaran shugaban kasar, ya duƙufa na wurin ganin ya amshi mulkin Nijeriya domin cigaba da yaɗa manufarsa na Alheri.”
Atiku Abubakar yasha alwashin kawo ƙarshen zaman banza da matasa ke fama da shi, na karancin aikin yi wanda hakan ya biyo bayane Sakamakon rashin jari, to h ɗan takaran ya tsaya tsayin daka domin amsa mulkin Nijeriya ya yaɗa manufarsa na ganin matasa sun ci gajiyar mulkinsa.”