Dan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kwarin gwiwa kan nasarar da ya samu a jihar Anambra, a zaben 2023.
Wannan shine matsayin ɗan takarar a yayin wani atisayen daidaita ƙungiyoyin tallafi sama da 200 a jihar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na tikitin Atiku-Okwa a jihar Anambra, karkashin jagorancin Darakta Janar na kungiyar Farfesa Obiora Okonkwo.
Okonkwo ya bayyana kwarin gwiwar cewa Atiku Abubakar da Sanata Ifeanyichukwu Okowa, za su samu rinjayen ƙuri’u a jihar Anambra idan aka yi la’akari da irin goyon bayan da aka samu daga Ndi Anambra.
Okonkwo ya bayyana haka ne a Awka, jihar Anambra, bayan taron kwamitin gudanarwa na jihar. Ya yaba da kwazon aiki, jajircewa, da sadaukarwar mataimakin darakta a ƙungiyoyin tallafi da sa kai Rt. Hon. Onyebuchi Offor, wanda kuma shine shugaban marasa rinjaye a majalisar jihar Anambra ta bakwai.
Ya ce: “Ba mu da tantama jihar Anambra za ta ba PDP kuri’u masu rinjaye; wannan ya ci gaba da zama kamar yadda aka saba tun 1999. Mu dai mun ci gaba da zama a jam’iyyar PDP ko da akwai wata jam’iyya a matakin jiha, amma jama’a sun ci gaba da zabar jam’iyyar ta kasa mai yaduwa da karfin da za ta iya lashe zaben shugaban kasa.
Rahoto: Shamsu A Abubakar Mairiga.