Shugaban mata APC ta kasa ta yi Alkawarin haɗawa Tinubu kuri’u miliyan 40..
Shugabar matan APC ta ƙasa, Betta Edu, ta sha alwashin haɗa wa Bola Tinubu kuri’u 40 na matasa da mata a zaɓen 2023.
Misis Edu tace gwamnatin Bola Tinubu da Shettima zata sa bukatun mata a gaba kamar yadda suka yi a jihohinsu.
Matar Tinubu ta roki mahalarta gangamin a Kalaba jihar Kuros Riba ta roki kowa ya karbi PVC su zabi APC a 2023.
Calabar, Cross River – Shugabar matan jam’iyyar APC ta ƙasa, Betta Edu, ta kudiri aniyar tara wa dan takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kuri’u miliyan 40 a babban zaɓen 2023.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Edu ta ɗauki wannan alƙawarin ne a Kalaba, babban birnin jihar Kuros Riba a wurin gangamin mata da matasa na kudu maso kudu.
Tace ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC da abokin takararsa, Kashim Shettima, sun zuba wa al’umma aiki lokacin suna matsayin gwamna a jihohinsu.
A cewar Misis Edu, rawar da suka taka a jihohinsu ta kai a sake basu dama su kara yi wa al’ummar Najeriya aiki a matakin ƙasa.
“Ɗan takarar shugaban ƙasa na APC babban mai son ci gaban mata da matasa ne don haka ya cancanci samun tulin goyon baya da kuri’unsu. Tinubu ya taimaka wa mata kuma mun gani a ƙasa.”
“Ya goyi bayan matarsa wacce take Kirista har ta kai matsayin Sanata da wasu mata a jiharsa (Legas). Idan kuka koma jihohinku, ku shiga lungu da sako ku tattara wa APC masoyan da zasu zaɓi Tinubu/Shettima.”
“Ku tabbata kun karbi Katin zabenku sannan ku garzaya runfunan zaɓenku ku dangwalawa Bola Tinubu a watan Fabrairu, 2023.”
Betta Edu, A nata jawabin, Oluremi Tinubu, mai ɗakin dan takarar shugaban ƙasa na APC, ta roki matan kudu maso kudu a babban zaɓen 2023 saboda zasu amfana sosai a mulkin mijinta.
“Mun shirya ba mata muhimmanci a gwamnatin gaba da izinin Allah, zaben Tinubu/Shettima zaɓi ne na cigaba, zata buɗe wa matasa su samu dama kuma ta dawo da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.”
Haka zalika mai ɗakin gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Riba, Linda Ayade, ta roƙi mazauna jihar su mallaki katin zaɓe kuma su dangwalawa APC a zaɓen watan Fabrairu mai zuwa.
Rahoto: Zuhair Ali Ibrahim.