Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada cewa rayukan ‘yan Najeriya za su fi garantin samun kyakkyawar kulawa a hannun APC fiye da sauran jam’iyyu masu takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke rantsar da Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Bola Tinubu, a Abuja.
Buhari ya ce ya zama wajibi a yi duk irin ƙoƙarin da ya dace domin a ga APC ta ci gaba da mulki, yadda ‘yan Najeriya za su ci gaba da cin alherin da APC ta kawo a ƙasar nan.
Yayin da ya ke jinjina wa ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, Buhari ya kuma jinjina wa dukkan sauran ‘yan takarar da su ka yi zaɓen fidda gwani tare da Tinubu, amma su ka janye masa, ko kuma ya kayar da su.
Ya ce babu wata jam’iyyar da ta dace da ‘yan Najeriya sai APC.
Da ya ke jawabi, Tinubu ya jinjina wa Buhari da kuma gwamnatin sa, tare da cewa idan ya hau mulki, zai ɗora daga inda Gwamnatin Buhari ta tsaya.
An dai ƙaddamar da Daftarin Ƙudirorin APC, wato APC manifesto, mai shafuka 80, wanda cike ya ke da wasu alƙawurran da APC ta ɗauka tun a 2015, amma har yau ba ta cika ba.
Shugaban Kamfen ɗin TInubu 2023, Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato, ya ce ya zama wajibi duk wani ɗan kwamitin kamfen ya tashi tsaye wurjanjan ya yi aiki tuƙuru.
Ya ce zai wanda aka aza ƙoƙarin da ya yi a sikeli aka ga ya yi ƙwazo, kuma ya kawo sakamako mai kyau kaɗai za a yi wa kyakkyawar sakayya idan an yi nasara.
Ya ce ba zai yiwu a naɗa ɗan kwamiti amma ya je Abuja ya yi kwance ba. Ya ce kowa ya bazu cikin karkara, domin a can ne masu zaɓe su ke.
Za a yi zaɓen shugaban ƙasa a ranar 25 Ga Fabrairu, 2023.