Jam’iyyar “New Nigeria Peoples Party” Mai alamar kayan gwari ta ce ɗan takararta na shugaban ƙasa, Dakta Rabi’u Kwankwaso, ba zai janye wa takwaransa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ba.”
Kakakin jam’iyyar NNPP, Manjo Agbo, wanda ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da daya daga cikin wakilanmu, ya yi zargin cewa shugabannin Arewa na tursasa Kwankwaso ya sauka domin Atiku.”
Da yake mayar da martani ga rahoton, Agbo, ya yi tambaya, “Ta yaya wani zai fito ya ce Kwankwaso ya sauka domin Atiku? A’a Atiku ne ya kamata ya sauka.”
“A cewarsa, Kwankwaso na cikin fafutukar samun nasara, yana mai jaddada cewa shi ne zai zama shugaban kasar.
Sai dai kakakin jam’iyyar NNPP bai yi watsi da yiwuwar tattaunawar ƙawance ba, wanda ya ce za a yi a bisa sharuɗɗan da ta kayyade.”
Da aka tambaye shi game da batun tattaunawar da ake zargin jam’iyyarsa da kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Agbo ya yi watsi da rahoton.
“Je ka tambayi Okupe (Dr Doyin Okupe). Shi ne wanda ya yi watsi da maganar kawancen farko saboda ya shigatattaunawa da ajandar sa ta ‘ba saba’ ba cewa a nada Obi a matsayin shugaban kasa.
Haka kuma, Shugaban NNPP na ƙasa, Rufai Alƙali, shi ma ya bayyana ra’ayin Agbo a matsayin wanda ba gaskiya ba ne.
Alƙali, Farfesa a Kimiyyar Siyasa ya ce rahoton na hannun wasu mutane ne da suka himmatu wajen yaudarar ‘yan Najeriya wajen samun maki na siyasa mai arha.
Ya ce, “Gaskiya karya ce. Ba mu yi mamakin cewa wannan labarin yana fitowa haka ba a wannan lokacin, Duk ’yan Najeriya masu hankali sun bi wannan tsari na Jam’iyyar NNPP.
Da farko sunce ɗan takarar zai marawa Asiwaju baya, Da muka karyata hakan, sai suka ce NNPP ta miƙa wuya ga jam’iyyar “Labour da Peter Obi, Da muka yi bayanin halin da ake ciki, sai suka yi shiru.
“Bayan haka, akwai wani yunƙurin da dattawanmu suka yi a taron tattaunawa na Arewa Consultative Forum na ‘yan takarar shugaban kasa su gabatar da takardunsu.
Mun amince da masu shirya taron amma mun fahimci cewa akwai dakarun da ke aiki don lalata tsarin ta hanyar amfani da dandamali wajen amincewa da ɗan takarar Arewa duk acewar Jam’iyyar NNPP ɗin, bisani Lokacin da Kwankwaso bai bayyana a wurin taronba ba, wannan aikin ya ruguje.
“A makonnin da suka gabata, ɗan takarar ya gabatar da tsarinsa wanda ya fito sosai Ya kasance a muhawarar shugaban kasa ta AriseTV -CDD wacce ta yi nasara sosai.
Ya yi tattaki zuwa Kudu-maso-Gabas, ya yi kwanaki uku a Enugu da Abakiliki, Duk waɗannan nasarorin da aka samu, tsoro ya kawo su tare da yadda za’a magancesu.”
Yanzu sun fito da wani lamari da ake matsa masawa kwankwaso ya sauka domin marawa Wata jam’iyya baya, Sauka don wa? A wani yanayi? Shin a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya ta faru cewa ɗan takarar shugaban kasa da jam’iyya mai karfi ke mara masa baya, ‘yan Najeriya suka yi masa kirari da ya cigaba, zai mika tsarinsa ga wani?
Farfaganda ce da yaƙin tunani kuma duk wadanda ke da hannu a wannan lamarin ya kamata su daina.”
Daga Salman Ibrahim Ɗan-ma’azu Katsina.