“A daren jiya, Ɗan takaran shugaban kasar Nijeriya ya jagoranci tawagarsa tare da Ɗan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa, Dr. Ifeanyi Okowa, inda muka kai ziyarar ban girma ga tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan a gidansa dake Abuja.
Ɗan takaran shugaban ƙasar Nijeriya ƙarƙashin jam’iyar PDP, ya kai ziyarar bangirma ga tsohon shugaban kasar Nijeriya “Good Luck Jonathan” har gidansa dake birnin Abuja.”
“Tsohon shugaban kasar Jonathan, ya ji daɗin wannan ziyarar da tawagar Atiku Abubakar suka kai masa har gidansa, inda tsohon shugaban kasar ya yaba da manufofin Atiku Abubakar ɗin tare da yiwa Ƴan Nijeriya sha’awar cewa Atiku Abubakar ya zama Shugaban ƙasar Nijeriya.”
Jonathan ya tarba Ɗan takaran shugaban kasar cikin girmamawa tare shirya masu liyafar bangirma a cikin Wannan dare.”
“Atiku Abubakar ya ƙara jaddadawa tsohon shugaban kasar irin manufofin gwamnatinsa daga lokacin da aka ce an rantsar da shi matsayin shugaban kasar Nijeriya bayan lashe baban zaɓe.”