Na Samu Miliyan 35 Daga Babana A Matsayin Kyautar Aure Amma Ban Sanar Da Mijina ba.
Wata sabuwar matar aure mai Suna Mummy Ikke Haifafiyar Jahar Legas ta bayyana cewa ita da mijinta suna da sabani kan kudin da ta karba a matsayin kyautar auren mahaifinta.
Ta yi ikirarin cewa mahaifinta ya ba ta dala miliyan 35, amma ba ta taba gaya wa mijinta kudin ba har sai da ya gano su da kan sa.
A cewarta, dukkansu sun fito ne daga iyalai masu hannu da shuni, don haka ba ta ga wani laifi ba wajen gaya wa mijinta, wanda shi ma ya fito daga dangi masu arziki.
Lokacin da yake samun matsala da manhajarsa na bankin kuma ya nemi ya yi amfani da nata, ya gano miliyan 35.
Sai da ya ganta sai ta bayyana daga wajen mahaifinta ne, amma sai ya yi mamakin cewa tana da irin wannan kudi amma ba ta taimaka masa a lokacin da ake bukata ba.
Matar ta ce mutumin nata ya ji takaici musamman saboda akwai lokacin da suke son siyan gidan da ya fi kasafin kudinsa duk da haka tana da wannan adadin amma ba ta taba yin tayin kammala biya ba.
Ta nemi shawarar yadda za ta nemo mafita daga matsalar da ta tsinci kanta dangane da sirrin da ta boye ga mijinta.