Daga Salma Ibrahim Dan-ma’azu Katsina
Wani jigo a jam’iyyar PDP a jihar Ogun, Segun Showunmi, ya yi kira ga tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo da kada ya yi watsi da kasar nan yayin da take sauya shugabancinta a zaben 2023 mai zuwa.
Showunmi ya yi wannan roko ne a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Litinin, inda ya kara da cewa a matsayinsa na kwararre mai kishin Afirka, ya kamata Obasanjo ya ba da taimako da shawarwari masu matukar kima ga ‘yan kasa.
Ya ce “yana tare da miliyoyin jama’a, musamman ‘yan kasar Habasha wajen mika godiyar ku ga Obasanjo kan kokarin da yake yi na magance rikicin kasar Habasha da ya addabi wannan ƙasa ta Afirka tsawon shekaru da dama.