Ɗan takaran Shugaban ƙasar Nijeriya Alh. Atiku Abubakar wazirin Adamawa, a yau ne ya sauka jihar kwara a Domin ƙaddamar da manufofin yaƙin neman zaɓensa.”
Jihar Kwara ta yi maraba da tawagar mu tare da mai da hankali a dandalin Metropolitan, Ilorin, domin sauraren kyawawan manufofin mu inji Atiku.
Sakon takaici ne ga jam’iyyar APC da kuma tabbacin dawowar jam’iyyar PDP. A matsayin masu cigaba da gudanar da mulki.
Atiku Abubakar ya ƙara da cewa a cikin jawabinsa, yayi farin ciki da ganin yadda mata da miliyoyin ke nuna goyon bayan takaransa.
Ɗan takaram shugaban ƙasar Nijeriya ƙarƙashin jam’iyar PDP Alh. Atiku Abubakar ya amshi tawagar ƙungiyar mata masu yaƙin neman zaɓsnsa tare da tawagar miliyoyin masoyansa a jihar kwara.
Ɗan takaran Shuagaban ƙasar Nijeriya Atku Abubakar yace, Zai dawo da martabar Najeriya kamar a wancan lokacin.
Za kuma mu buƙaci tuntuɓar duk masu ruwa da tsaki a cikin ƙasarmu, musamman kan abinda ya shafi Addinin Islama da na kiristancin.
A don hakan gwamnatin mu za ta yi ƙoƙarin ganin haɗin kan al’umma, ta yadda za su yi haɗin gwiwa da “Ecumenical Centre” da ke Abuja don tattaunawa ta da kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN).
Yayi alƙawarin zama zance mai ƙarfi da gamsarwa ma ganin Nijeriya ta samu haɗin kai mai ƙarfin gaske tare kawo ƙarshen matsalolin tsadar rayuwa.”