A Kano Budurwa takai karan saurayinta kotu bisa zargin yada tsaraicinta a fesbuk.
Wata budurwa a kano ta maka saurayinta kotun shari’an musulunci kan barazanan yada hoton tsaraicinta a fesbuk.
‘Yan sandan jahan sun gurfanar da matashin a gaban kotu a unguwam Gama PRP a karaman hukuman Nasarawa don karban hukunci akan laifin da ya aikata.
Wata majiya ta rawaito cewa, mai gabatar da karan Aliyul Abidin ya shaida ma kotu cewa ana zargin matashin da bata ma budurwan suna bayan yayi mata barazanan yada hoton tsaraicinta a fesbuk wanda wanda hakan na iya bata mata suna.
Tunda farko saurayin yayi ma budurwan barazana ne don ta saya mishi waya ita kuma taki saya.
Kotu ta yanka ma saurayin tara maiyawa bisa laifin daya aikata.
Sai tausayi ya kama budurwan inda tace ta janye karan da ta shigar akan saurayin nata.
Saidai bayan janye karan nata kotun ta sallami matashin da ake tuhuma, inda ta gargadeshi kan yima mutum barazana.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.