A Legas Saurayi ya kashe budurwansa dalili don ta juya masa baya bayan ta ci kuɗinsa .
Saurayi ya kashe budurwan shi saboda ta gujeshi bayan ya nema mata aiki a legas.
Ko wadanne masoya na fukantar gwaji kowane lokaci don gane irin girman soyayyansu, Amma hakan bai hanasu son juna ba.
Wani lokaci muna shiga soyayya ba tare da komaiba, kuma abokan soyayyan mu suna taimaka mana muzama wani abu a rayuwa.
Babban abun bakin cikin shine mafiyawan lokutan da muke samun wadannan abubuwan alherin muna godewa mutanen da suka taimaka mana.
Wannan shine abinda ya faru ga wasu masoya guda biyu, inda dayan ya temaka ma daya daga baya suka rabu.
Wannan masoya guda biyu da suke zaune a garin lagos, sunyi suna sosai a fagen soyayya, inda kowa yasansu tare.
Saboda tsananin shakuwa da soyayya, yasa komai shine yakeyi mata inda har ya bata lasisin fasfo.
Saurayin yayi shige da fice harta zama mafi kyau da ban sha’awa ga mutane.
Saurayin Ya nema mata aiki a wani babban kamfani, inda take daukan albashi mai yawan gaske.
Kwasam sai suka samu sabani, inda hartakaisu ga rabuwa, Hankalin saurayin ya tashi sosai, inda ita kuma taki sauraren shi, Kawai sai ya yanke shawaran kasheta, tunda yabata komai na rayuwa amma tajuya mishi baya.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.