A shirye na ke kan binciken EFCC na kasa, cewar Gwamnan Benue Ortom.
Daga: Shamsu S Abbakar Mairiga.
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya sha alwashin ba zai tsere ma hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ba, lokacin da aka bukaci ya bayar da bayanin yadda ya kashe kudaden jihar sa.
Da yake jawabi a zaman majalisar ministocinsa da aka yi a tsohon dakin liyafa na gidan gwamnati, Makurdi, Ortom ya ce shi ba matsoraci ba ne. Ya bukaci ‘yan majalisarsa da kada su sanya tsoro a duk lokacin da EFCC ta gayyace su domin amsa tambayoyi.
Yace; Duk lokacin da EFCC ta gayyace ka, kada ka ji tsoro ka tafi, ni ba matsoraci ba ne in gudu daga EFCC, idan sun zo nemana zan bi su.
“Ba ni da wani jari a Turai duk abin da nake da shi a wannan jihar. Idan na aikata wani laifi bari mutum ya zo ya nuna mini.”
Da yake nasa jawabin, Ortom ya godewa ‘yan majalisarsa bisa gudunmawar da suka bayar wajen nasarorin da gwamnatinsa ta samu a cikin shekaru takwas da suka gabata. Ya kuma gode musu da yaba masa tare da yi alkawarin tabbatar da cewa sun ci gaba da kulla alakarsu.