Karo na uku ke nan a jere tawagar Super Eagles na shan kashi…
Tawagar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles ta ci gaba da taka ƙazamar rawa a ƙarƙashin mai horarwa Jose Peseiro bayan Portugal ta casa ta da ci 4-0 ranar Alhamis.
‘Yan wasan Najeriya sun ɗan farfaɗo bayan dawowa daga hutun rabin lokaci bayan wasan Portugal ɗin ta mamaye kashin farko.
Tawagar Selecao ta katange ‘yan wasan Super Eagles a kashin farkon, inda Super Eagles suka buga shot ɗaya kacal.
A ɗaya hannun kuma, Bruno Fernandes da Joao Felix ne suka bai wa Najeriya wuya a wajen kai hare-hare yayin da Bernardo Silva ya dinga haddasa abin da ya saba daga tsakiyar fili.
Hakan na nufin Jose Peseiro ya yi nasara a wasa biyu kacal da ya jagoranci Najeriyar tun bayan da ya karɓi aiki a watan Mayun da ya wuce.
Duk da cewa wasannin sada zumunta ne, rashin nasara akai-akai ka iya harziƙa magoya baya waɗanda ke son a yi nasara ko ma a wane irin wasa ne.
Tun a minti na 9 da take wasa Buruno Fernendez ya jefa wa Najeriya ƙwallo kafin ya jefa ta biyu a bugun finareti a minti na 35. Sai a minti 10 na ƙarshen wasa Ramos da Mario suka biyun.
Masu bi da kuma sharhin wasanni na ganin tawagar Najeriya ba ta nuna tana da wani tsari ko kuma manufa da take bi ba a wasan na Alhamis.
Kazalika, ƙarancin fahimtar juna ya sa ‘yan wasan ba sa murza leda a tsakaninsu yadda ya kamata, a cewar wani mai sharhin wasanni Anas Tukuntawa.
“Kamar ‘yan wasan baya William Troost-Ekong da Kevin Akpoguma, akwai ƙarancin fahimtar juna a tsakaninsu,” in ji shi.
“Haka ma Wilfred Ndidi, kamar bai san abin da yake bugawa ba. Shi kuma Alex Iwobi yakan kai ƙwallo gaba amma sai a rasa yadda ‘yan wasan gaba za su yi da ita.”
Me zai faru da a ce Najeriya za ta buga Kofin Duniya?
Wannan ne karo na biyu da Super Eagles ke rasa gurbin shiga gasar Kofin Duniya tun bayan da ta fara zuwa a shekarar 1994.
Cikin gasa takwas da aka yi a baya, Najeriya ta gaza zuwa na 2006 da 2022 ne kawai.
Da ma can ba a tsammanin zaratan ‘yan wasan na Super Eagles za su fi na Portugal taka rawa a wasan amma ba a yi tunanin za kwashi ruwan ƙwallaye ba.
“Gaskiya da a ce za su buga Kofin Duniya kuma suka yi rashin nasara da ci 4-0, zan ce ba za su yi abin da ya kamata ba saboda Juma’ar da za ta yi kyau daga Laraba ake gane ta,” in ji Tukuntawa.
Ya ƙara da cewa yana ganin ba za su wuce zagayen farko ba.
“Kodayake dai da ma haka wasan Najeriya yake kasancewa. Suna iya samun matsala a wasan sada zumunci amma kuma sai ka ga sun yi kyau a gaba.
“Ko a gasannin baya ma za ka ga ba su yi ƙoƙari a wasannin farko ba, sai daga baya kuma ka ga sun taɓuka abin kirki.”
Najeriya ba za ta sake buga wani wasa ba har sai 20 ga watan Maris na 2023, inda za ta nemi gurbin shiga gasar Kofin Ƙasashen Afirka da Guinea-Bissau a gidanta.
Mako guda bayan haka kuma a buga zagaye na biyu na wasan a ƙasar Guinea.
Daga Zuhair Ali Ibrahim.