Aboki Ya Yi Awon Gaba Da Matar Abokinsa Amarya Ana Tsaka Da Shan Shgalin Biki.
Wani matashi ya fada soyayya da budurwar abokin shi bayan ya nemi da ya samar mata da gidan da za ta zauna
Wani mai amfani da Twitter @MichaelJaQson, ya bayyana cewa shekara shida da suka wuce, ya nemi abokinsa da ya samarwa budurwarsa wacce ta yi tafiya zuwa Kigali, gidan zama
Sai dai, yadda ya so ba haka ta kasance ba, inda abokin na sa ya bige da soyayya da budurwarsa, yanzu har sun shekara biyar da aure
Wani matashi ya bayyana yadda abokinsa ya aure masa budurwa bayan ta yi tafiya zuwa birnin Kigali na kasar Rwanda.
Wani mai amfani Twitter,@MichaelJaQson, ya ce ya roki abokinsa da ya taimaka ya taya budurwarsa neman gidan da za ta zauna.
Michael ya bayyana cewa abubuwa sun juye inda abokin na sa ya fara soyayya da budurwarsa. Yanzu har sun yi shekara biyar da aure.
Matashin ya kuma yi habaici ga gajerun mata, inda ya ce shi yanzu tsoron su ya ke yi.
“Budurwar da na yi soyayya da ita shekara shida da suka wuce ta yi tafiya zuwa Kigali. A matsayina na saurayi mai nuna kulawa, sai na kira daya daga cikin abokaina da ya ke a can, ya taimaka mata ta samu gidan da za ta zauna mai kyau. In takaice mu ku labari dai yanzu shekarar su biyar da yin aure.”
Sharhin Jama’a
@Ninosongz said:
“A bangaren kwallon kafa, wannan shi mu ke kira da aro na tsakiyar kakar wasa da zabin siya dan’uwa. Abin takaici ne, amma ina tunanin ka manta inda ya kamata ka ji tsoron mutane irin abokinka. Ya fi budurwar ka da ta juya maka baya hadari.”
@optimis0 ya rubuta:
“Ƴanmata su ne misali mai kyau na abinnan da aka cewa ‘idan abinda kake so bai samu ba, sai abinda ya samu ya zama wanda kake so’.”
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim