Abunda yasa Akpabio ba zai iya zama shugaban majalisar dattawa ba.
Kakakin majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party, Daniel Bwala, ya bayyana dalilan da suka sa ba za a zabi Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa ba.
Bwala ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a safiyar ranar Litinin.
Ku tuna cewa Akpabio, tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, jam’iyyarsa ta APC, ta tsayar da shi a matsayin shugaban majalisar dattawa ta kasa ta 10.
Tsohon gwamnan dai na fuskantar zazzafar takara daga Sanatoci, Ali Ndume, Orji Uzor Kalu, da Jibrin Barau, da dai sauransu.
A cikin sakonsa na twitter, Bwala ya ce yunkurin Akpabio na yin takarar shugabancin majalisar na da cikas da kalubale masu yasa.
Bwala ya rubuta, “Ba za a zabi Godswill Akpabio a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa ba. Gajimaren da ya taru akan burinsa yana da nauyi da kauri. Ba addini ne ya zaburar shi ba, a’a bangaranci ne da kuma ramuwar gayya ta kawancen dukkan makiya. Yawancin Sanatocin da ke bin sa ba sa tare da shi.”
Rahoto: Kamal Aliyu Sabongida