Adireshin Imel Yanzu Wajibi Ne Domin Yin Rijistar UTME – JAMB
Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta sanar da cewa daga ranar 31 ga watan Junairu, 2023, babu wani maison rubuta jabawar da za a yi masa rajistar JAMB ba tare da samar da adireshin IMEL ba.
Hukumar ta lura da cewa duba da shawarar ta kan rajistar UTME da ke gudana shine don tabbatar da cewa an bi ingantattun hanyoyin da za a bi wajen kamo duk bayanan da suka shafi masu buƙatar shiga.
Ta ƙara da cewa sabuwar Shawarwari kan taimakawa wajen fitar da bayanai masu dacewa da na zamani na masu son shiga , kuma yana da matukar muhimmanci wajen saukaka watsa hanyoyin sadarwa na gaggawa da mahimmanci ga ɗaliban cikin arha da inganci.
Shugaban sashen hulɗa da jama’a na hukumar ta JAMB, Dakta Fabian Benjamin, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin ɗin da ta gabata, ya ce adireshin imel na samar da sassaucin ra’ayi a fannin sadarwa kuma hanya ce ta ƙwarewa wajen tuntuɓar masu buƙatar
“Saboda haka, ana shawartar ’yan masu buƙatar JAMB da su samu sahihan adiresoshin imel kafin su ci gaba da yin rajistar UTME.
“Bugu da ƙari, su tabbatar da cewa an adana kalmomin sirrinsu amintacce saboda Hukumar ba ta dawo da kalmar sirri ta imel ba ko canza adireshin imel da zarar an yi rajista,” in ji shi.
RAHOTO:– Comrade Yusha’u Garba Shanga