Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce aikin hakar mai a filin Kolmani da ke tsakanin Gombe da Bauchi ya jawo jarin dala biliyan 3.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata jim kadan kafin ya tashi daga aikin mai.
Shugaban kasar ya kuma ce ana ci gaba da kara gano mai a yankin Anambara da karamar hukumar Binuwai da sauran sassan kasar nan.
“Wannan binciken ya samo asali ne daga cajin da muka yi wa NNPC don sake tsarawa tare da fadada sawun binciken man fetur da iskar gas zuwa kan iyakar Anambra, Dahomey, Sokoto, Benue, Chadi da Bida Basins. A halin yanzu dai ana ci gaba da gudanar da irin wannan ayyuka a fadin sauran kwanduna.
“Mun gamsu da yadda aka gano sama da ganga biliyan 1 na man fetur a yanzu da kuma Kubik Feet na Gas biliyan 500 a yankin Kolmani da kuma yadda ake samun karin kudaden ajiya yayin da muke kara kaimi wajen binciken.
“Saboda haka abin yabo ne ga wannan gwamnati cewa a daidai lokacin da babu sha’awar zuba jari a makamashin burbushin halittu, tare da kalubalen wurin, mun sami damar jawo jarin sama da dala biliyan 3 kan wannan aikin,” in ji shi.
Dangane da amfani da filin na Komani, Buhari ya ce: “A matsayin aikin ci gaba mai cike da hadin kai wanda ya hada da samar da ruwa, tace man fetur, samar da wutar lantarki da taki, aikin ya yi alkawarin fa’ida da dama ga kasa. Wannan ya hada da amma ba’a iyakance ga Tsaron Makamashi ba, Tsaron Kudi, Tsaron Abinci da kuma ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin kasa baki daya.”
Ya kuma ce gwamnonin jihohin Bauchi da Gombe sun ba da tabbacin jajircewa da kuma aniyarsu na tabbatar da goyon baya da hadin kai a wadannan kananan hukumomin domin wannan aiki ya shafi al’ummar yankin.