A karon farko Zahra Buhari ta wakilci A’isha Buhari a taron kamfe na Tinubu a kalaba.. A
Mata sun cika wajan gaggamin Bola Tinubu Matar Shugaban kasa bata iya zuwa ba.
Tawagar matan da ke yakin neman zabe a jam’iyyar APC sun yi gagarumin taron kamfe a Kalaba.
Zahra Buhari ta wakilci Aisha Buhari a taron, amma an ga fuskokin Remi Tinubu da Nana Shettima.
Matan sun kai ziyara zuwa fadar Edidem Ekpo Okon Abasi Otu V, sun yi kira da a zabi APC a 2023.
Cross River – Mutane da-dama suka fita ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba 2022 zuwa babban gangamin matan APC na yankin Kudu maso kudu.
Jaridar Punch tace an yi wannan babban taron yakin neman zabe na Bola Tinubune a filin wasan U.J Esuene a garin Kalaba da ke jihar Kuros Riba.
Matar ‘dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar APC, Oluremi Tinubu ta halarci gangamin tare da mai dakin Kashim Shettima, Nana Shettima.
Taron ya samu halartar matan manyan ‘yan siyasa a Najeriya, amma jagorar tafiyar mata, Aisha Buhari ba ta iya zuwa ba, sai dai ta aika da wakilci.
Zahra Buhari-Indimi ta wakilci Mahaifiyarta a garin Kalaba dauke da gwagwaro mai tambarin APC.
Rahoton yace tawagar ta ziyarci Mai martaba Obong na Kalaba, Edidem Ekpo Abasi Otu V inda ta kai masa ziyarar ban girma kamar yadda aka saba.
A madadin uwargidar shugaban Najeriya, Zahra Buhari-Indimi ta gabatar da jawabi tana mai fatan matasa da mata su kawowa APC nasara a zaben badi.
Zahra Buhari take cewa jam’iyyarsu ta tsayawa zaman lafiya da cigaba, don haka tayi kira ga duk wani matashi da wata mace su taya su yakin neman zabe.
Ita kuwa Sanata Oluremi Tinubu, ta yabawa matan Kudu maso kudancin Najeriya, tayi alkawari za a kula da matasalar mata idan aka zabi mai gidanta.
Leadership ta fitar da rahoto cewashugabar matan jam’iyyar APC ta kasa, Dr. Betta Edu wanda mutumiyar jihar ce,tayi kira ga mata su mara masu baya.
Uwargidar gwamnan Kuros Riba, Dr. Linda Ayade tana wajen a yayin da aka rabawa mata tutoci.
Rahoto: Zubair Ali Ibrahim.