ALFIJIR HAUSA Ta Dakatar Da Wani Ma’aikacinta Bisa Kamasa Da Laifin Yin Ƙage.
“Amadadin masu ruwa da tsaki na wannan kamfanin Dillancin Labarai ta ALFIJIR HAUSA ta dakatar da ɗaya daga cikin editocinta Shamsu Ashafa sakamakon kamasa da laifin ruwaito labari wanda ba haka ba.
“Idan ba ku manta ba jaridar ta wallafa wani labari a jiyan dangane da wani fitaccen mai bada maganin gargajiya wanda ya yi shura a fagen yin addu’a domin cire aljanu wato malam Ibrahim Bilhaƙƙi.
Biyo bayan yadda rahoton ya fito an samu algushi a ciki, inda muka bibiya lamarin tare da yin kaciɓus da akasin gaskiyar al’amari.
“A don haka ne ALFIJIR HAUSA ta dakatar da shi, kuma ta nemi da ya gagauta miƙa shaidar lasisin aikinsa da Jaridar wato “ID Card” ga ita kamfanin.