Alhazai da dama sun jikkata Sakamakon hatsari a mota da ya rutsa da su a Nasarawá.
Mutane da dama sun jikkata yayin da wata motar bas mai jigilar Alhazan Saudiyya ta yi hatsari a Abuja
Wata motar bas mai kujeru 18 da ke jigilar maniyyatan Saudiyya daga jihar Nasarawa zuwa Abuja ta yi hatsari a ranar Laraba a kan hanyar Kara, Keffi zuwa Abuja.
Wani shaidar gani da ido ya shaida wa manema labarai cewa, hatsarin ya afku ne a kusa da Kara, karamar hukumar Keffi, jim kadan bayan wata motar bas mai mutane 18 da ke jigilar maniyyatan ta taso daga Nasarawa zuwa Abuja.
Babu wata sanarwa a hukumance da hukumar alhazai ta fitar kan lamarin.
Har yanzu babu cikakken bayani kan hadarin amma an tattaro cewa wasu mutanen da ke cikin motar sun samu raunuka daban-daban kuma an kai su asibiti domin kula da lafiyarsu.
Sai dai ba a bayyana ko an samu asarar rayuka ba har ya zuwa lokacin da ake cika rahoton.
Rahoto Kamal Aliyu Sabongida