Sabuwar Amarya ta shiga zubda hawaye yayin da wanda ta aura yace ya fasa aurenta a gaban kowa.
A kan hanyar komawa gida daga Majami’a, Mijin ya yi amai ya lashe ya soke batun aurensu a ranar ɗaura aure.
Duk da kokarin Amarya da sauran waɗanda abun ya faru a gabansu na shawo kan Saurayin, sam ya ƙi sauraronsu.
Wani ɗan Najeriya dake shirin Angoncewa ya bar mutane baki buɗe bayan ya canza shawara, ya fasa auren kyakkyawar amaryarsa a ranar ɗaura aure.
A wani bidiyo da aka wallafa a soshiyal midiya, an jiyo muryar angon na faɗin ya fasa wannan auren, ya bayyana cewa ba zai koma gida da ita ba.
Nan take hawaye masu zafi suka fara sauka a kumatun amaryar yayin da ta bi shi tana rokonsa, amma matashin saurayin ya ƙeƙashe kasa kan ba zai canza ra’ayinsa ba.
Mutanen da abun ya faru a gabansu sun yi iya bakin kokarinsu na lalubo hanyar maslaha tsakanin masoyan amma duk a banza saboda Saurayin ya ɗau zafi kan matakin da ya ɗauka.
Haka zalika ya ƙi faɗin laifin da aka masa ya jawo ya yanke wannan tsattsauran matakin lokaci ɗaya.
Mutane sun maida martani
Patrick Solomon yace:
“Dan Allah karku kunyata bakinku da suka zo daga kusa ko nesa, ku basu abinci da kayan sha, duk abinda kuka ga dama zaku iya aikata wa bayan auren.”
Muhammad Umar yace:
“Ku bar baƙi su ci Shinkafa da nama kafin ku rabu, zaku iya raba hanya idan kuka koma gida, haba meke faruwa ne.”
Isi Olie tace:
“Anti ki hau mota ki koma gida abinki, meye na zubda hawaye kuma.”
Aliyu Malik yace:
“Ba haka nan, dole akwai wani ɓoyayyen sirri da ya gano a rayuwarta. Abu ya yi kyau.”
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim