An ƙaddamar da dandalin siyasa a Nijeriya ƙarƙashin Sheikh Ibrahim Al- zakzaky.
Dandalin Siyasa na Harkar Musulunci a Najeriya karkashin Jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky ya gudanar da taruka na tsawon kwanaki 3 a cikin gida da na kaddamarwar. (29 – 31 ga Oktoba, 2022).
Ƙungiyar ta kaddamar da ɗaruruwan mambobinta wadanda za su ɗauki nauyin gudanar da ayyukan ƙungiyar a shiyyar Arewa maso Gabashin ƙasar nan.”
“An gudanar da tarukan ne a jihohin Gombe da Bauchi. Wakilai daga jihohin Yobe da Borno da Adamawa da kuma Taraba na daga cikin wadanda suka samu jawabai masu zurfi a kan tsari da manufofi da ka’idojin da aka shimfida na dandalin. Wadanda suka halarci taron sun hada da Convener na kasa kodineta da sauran masu ruwa da tsaki na dandalin.”