An Bada Umarnin A Kamo Tsohon Gwamnar Kaduna Elrufa’i.
Wata Kungiya Ta Ba Da Umarnin Kwamishe Tsohon Gwamnan Kaduna Nasiru El-rufa’i Bisa zargin Fifiita Musulunci.
International Society for Civil Liberties and Rule of Law ta fito ta soki Tsohon Gwamnan Nasir El-Rufai.
Kungiyar ta na so a cafke tsohon Gwamnan Kaduna, ta zarge shi da fifita Musulunci a Najeriya.
Shugaban Intersociety, Emeka Umeagbalasi ya ce El-Rufai ya murkushe kiristocin Jihar Kaduna.
Wata kungiya International Society for Civil Liberties and Rule of Law da aka fi sani da Intersociety ta na so a damke El-Rufai.
Kamar yadda rahoto ya fito daga jaridar Vanguard a yau,kungiyar ta zargi tsohon Gwamnan jihar Kaduna da goyon bayan a musuluntar da Najeriya.
Intersociety ta ce Nasir El-Rufai ya na kira da aka kafa mulkin musulunci a Najeriya, wanda ke garaye da sauran Mabiya addinan da ba musulunci ba.
Shugaban wannan kungiya, Emeka Umeagbalasi ya zanta da manema labarai a garin Owerri a jihar Imo, inda ya jero wasu zunuban tsohon Gwamnan.
Mista Emeka Umeagbalasi ya jefi Malaman El-Rufai da neman jawo rikici tsakanin jama’a da kisan kare dangi da laifin tunzura al’umma da kalamansa.
Wannan kungiya mai neman tabbatar da bin doka ta ce tun ba yau ba ta ke jan hankali game da tsohon Ministan, sai a yanzu maganar ta fito fili.
“A wani faifen bidiyo, tsohon Gwaman Kaduna ya na kurin nasarar maida Kaduna kasar musulunci ta hanyar cigaba da rike mulki tun 2015.
An maimaita irin haka a Najeriya ta hanyar tsaida tikitin Musulmi da Musulmi a zaben shugaban kasa.
Intersociety ta saba bayyana irin yankan ragon da ake yi wa mutanen Kudancin Kaduna da Benuwai, Filato, Nasarawa, Kogi, Neja, Taraba da Adamawa.”
Rahoton ya ce Umeagbalasi ya yi ikirarin a shekarun nan, an hallaka mutane a Kudu maso yamma da Kudu maso gabashin Najeriya saboda bambancin addini.
Sai Dai har yanzu babu inda kungiyar nan ta Intersociety ta bada gamsassun hujjojin da ke tabbatar da irin kashe-kashen da yake cewa ana yi yankunan.
Intersociety ta ce a 2015 El-Rufai ya hana Kirista tikiti a zaben Gwamna, amma bincike ya nuna mataimakin Gwamnan jihar Kaduna a lokacin kirista ne.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim