An bawa hamata iska tsakanin Soja da Ɗan Sanda a bainin Jama’a a Legas.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa sojan da aka gani yana fada da wani dan sanda a ranar Laraba fasinja ne a cikin wata motar safa da ke tuki a kan hanya.
Bidiyon wani dan sanda da soja da ke fada a kan hanyar Legas ya bazu a ranar Laraba.
Da yake bayar da karin haske kan lamarin a ranar Laraba, Hundeyin ya ce sojan ya fusata ne saboda an tsayar da motar bas din da ke hana zirga-zirga, inda suka yi artabu da wani dan sanda dauke da makamai.
Hundeyin ya ce, “Sojan wanda fasinja ne, ya umurci direban da ya tuka motar, inda ‘yan sandan suka tsayar da motar, sai sojan ya yi fushi cewa an tsayar da motar da ya hau.
“Saboda haka ya yanke shawarar kai hari kan dan sandan da ke dauke da makamai, an sanar da Sojoji.”
Rahoto: Shamsu S Abbakar Mairiga.