An Cafke Dan Acaban Da Yaiwa Mai Juna 2 Fyade A Binuwe.
Daga Al-Asad Al-Amin Funtua
Jami’an rundunar ‘yan sandan jahar Benue, sun cafke wani direban babur dan shekara 40, mai suna Akpo Igwe, bisa zargin yi wa wata mata mai juna biyu fyade a unguwar Irabi, cikin karamar hukumar Obi, na jahar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jahar SP Catherine Anene, wacce ta tabbatar da kama Igwe a wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, ta ce an kama wanda ake zargin ne biyo bayan korafin da iyalan matan suka kai ofishin ‘yan sanda na Irabi.
“An kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da dangin matan suka bayar a ofishin ‘yan sanda da ke Irabi,” in ji ta.
A cewar rahoton, wacce aka yiwa fyaden mai ciki wata takwas, tana dawowa daga kasuwa ne ta tsayar da mai babur ya kai ta gida.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba 7 ga watan Yuni da misalin karfe 7 na dare. Akan hanyar su ne mai Okada ya karkata daga babban titin zuwa wani daji da ke kusa da titin, ya rike ta ya yi mata fyade.
sai ya yi tunanin ta mutu, sai ya fito da ita daga cikin daji ya jefar da ita a bakin kogi, inda ta kwanta har washegari inda ‘yan uwanta suka hau neman ta.
“An garzaya da ita asibiti cikin gaggawa yayin da aka kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda da ya kai ga cafke mai laifin.
Ta kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarnin a mayar da ‘karar zuwa hedkwatar ‘yan sanda da ke Markudi babban birnin jahar domin ci gaba da bincike.