Mutum Ya Musanta Yunkurin Satar Gawa Daga Makabarta.
Wani mutum da masu gadin makabarta suka kama a makon jiya a lokacin da ake zarginsa da yunkurin sace gawa a wani kabari a karamar hukumar Koko-Besse a jihar Kebbi, Yahaya Mamu, ya musanta aikata laifin.
Binciken ya gano tsakanin mazauna yankin ya nuna cewa lamarin ya dauki wani sabon salo biyo bayan musanta aikata laifin da wanda ake zargin ya aikata.
Mamu a wata sanarwa bayan kama shi, ya ce ya je makabartar ne domin gudanar da wasu gyare-gyare a kaburburan da ruwan sama ya lalata a lokacin damina.
A cewar wani dan kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa’ikamatusnnah [JIBWIS] da ba ya son a buga sunansa yayin da yake mayar da martani kan lamarin, irin wannan aiki sadaukarwa ce da ba ta bukatar izinin kafin gudanarwa da ita, kamar yanda Musulunci ya koyar.
Hakazalika, wani mazaunin garin, Abdullahi Idris Koko wanda ya yi magana game da kamun, ya ce irin wadannan ayyuka ba sa bukatar izini, ya kara da cewa a wajen Mamu masu kula da aikin ba su san manufarsa ba, sai da aka yi masa tambayoyi, sannan ya amsa cewa ya ziyarci makabarta kuma ya tona kasar kabari.
Koko ya ce ba aikin ma’aikatan makabartar ba ne su tantance wadanda suke kawo gawar don binne ko kuma daga inda ta fito, sai dai su rika sa ido kan motsi da kuma gyara makabartar.
Wakilin Leadership ya kasa samun ‘yan uwan mamacin da aka tona kabarin don jin ta bakinsu.
Jami’in ‘yan sanda reshen yankin ba ya kusa a lokacin da manema labarai suka ziyarce shi amma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, SP Nafi’u Abubakar, ya ce ba su samu labarin faruwar lamarin ba.
Rahoto: Kamal Aliyu Sabongida.