An Damke mamba a coci da laifin sace kayan sauti na wurin Ibadan a Osun.
An Damke Mutumin da Yayi Fashi a Coci, Dauke da Kayan da ya Kwasa.
‘Yan agajin kungiyar tsaro ta Amotekun sun yi ram da wani mutumi da kayan sata bayan ya yi fashi a wata majami’a
Mr Adewinmbi ya ce an kama mutumin da ake zargi da na’urar daukar murya, na’urar kara karfin murya, ganguna da sauran kayayyaki
Mazauna yankin sun yi kiran gaggawa ga ‘yan agajin Amotekun kan yadda suke zargin mutumin mai shekaru 47 da balle majami’ar, wanda hakan yasa suka hanzarta isa wurin
‘Yan agajin kungiyar tsaron yanki Amotekun na jihar Osun sun yi ram da wani mutumi mai shekaru 47 da ya kutsa cikin majami’ar Cheribum ta Seraphim cikin anguwar Ogo-Oluwa a Osogbo.
Bashir Adewimbi, birgediya-janar mai ritaya kuma kwamandan Amotekun na jihar, ya ce wanda ake zargin ya kutsa cikin majami’ar da misalin karfe 4:00 na safiyar Juma’a.
Ya shaida wa manema labarai a ranar Asabar yadda aka kama wanda ake zargin bayan wani mazaunin yankin ya sanar wa ‘yan agajin, jaridar TheCable ta rahoto.
” ‘Yan agajinmu sun samu kiran gaggawa daga mazauna Ogo-Oluwa cewa an balle wata majami’a, ana bukatar ‘yan agajinmu su hanzarta kama wanda ake zargin.
“Jami’anmu sun hanzarta daukar mataki, inda suka yi nasarar cafke wanda ake zargin yayin kokarin yin awon gaba da kayayyakin da ya sata a wurin.”
A cewarsa mr Adewinmbi ya ce an kama mutumin da ake zargi da na’urar daukar murya, na’urar kara karfin murya, ganguna da sauran kayayyaki, Premium Times ta rahoto.
Kwamandan ya ce an mika wanda ake zargin hannun ‘yan sanda don cigaba da bincike.
Ya bukaci mazauna yankin da su cigaba da samar da bayanan da zasu taimaka wajen cafke hatsabibai a jihar.
Ya kara da rokon mazaunan da su yawaita fallasa duk wanda suke zargi da mumanan ayyuka yankin.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.