An daure wani mutum na tsawon watanni 3 bisa samunsa da laifin satar injin nika.
Wata Kotun Majistare da ke Ota, Ogun, a ranar Litinin ta yanke wa wani matashi dan shekara 23, Opeyemi Ademola, hukuncin daurin watanni uku a gidan yari, bisa samunsa da laifin satar injin niƙa na Naira 70,000.
Rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da Ademola wanda ba a bayar da adireshin sa da laifin sata ba.
A hukuncin da ta yanke, Misis A O.Adeyemi, ta yankewa Ademola hukuncin biyan tarar Naira 5,000 bayan da ta amsa laifinsa.
Adeyemi ya kuma umarci mai laifin da ya biya N70,000 ga wanda ya kai karar.
Tun da farko, mai ba da shawara ga masu gabatar da kara, Insp E.O. Adaraloye ya shaidawa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 23 ga watan Maris a lamba 43, Ojuelegba, unguwar Arinko, Ota.
Adaraloye ya ce mai laifin ya saci injin nika ne daga hannun Hajiya Bashirat Adebuyi, bayan da ya dauke mata hankali kan zargin sayan kullun rogo na N300 (fufu).
Mai gabatar da kara ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 390(9) na kundin laifuffuka,Laws of Ogun,2006.(NAN)
RAHOTO -ZUBAIDA ALI TARABA