An Fara Amfani Da Mutum Mutumi Domin Rabawa Mutane Abinci a Otal.
Wani bidiyon da aka yada a TikTok ya nuna wani gidan cin abinci da babu alamar mutum, sai dai mutum-mutumi
Bidiyon ya nuna yadda wani mutum ya zo ya ba da odar abinci, mutum-mutumi ya dauko ya kawo masa kamar mutum
Ba sabon abu bane ganin irin wadannan abubuwa a kasashen waje, musamman yadda fasahar zamani ke kara yaduwa
A wani bidiyon da aka yada, an gano wani gidan cin abinci da kwastomomi ke odar abinci ta hanyar sanar da mutum-mutumi ba dan Adam ba.
Bidiyon da @notkevinlasean ya yada a TikTok ya nuna yadda gidan cin abincin mai suna Robot Restaurant da ke birnin Tokyo a Japan ke harkallarsa.
Bidiyon ya fara ne yayin da wani mutum ya kira mai kawo abinci; wanda yake mutum-mutumi tare da ba da odar nau’in abincin da yake bukata.
Daga nan bidiyon ya yanke zuwa wani wurin, inda aka nuna mutum-mutumin dauke da faranti cike da abinci ya nufi teburin da mutumin ke zaune.
Shi kansa kwastoman, ya yi mamakin yadda mutum-mutumin ke aiki cikin tsanaki ba tare da samun wani tsaiko ba.
Bidiyon dai ya dauki hankalin mutane da yawa a kafar sada zumunta, inda suke bayyana ra’ayoyinsu ga wannan fasahar.
Wannan dai ba sabon abu bane a birnin Tokyo, domin akan yi yawan karo da shagunan siyar da abinci da sauran wurare da dama da ke amfani da mutum-mutumi.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.