An fasa daura auren wata amarya saboda ansameta da cutan kanjamau a kaduna.
Rahotonni daga jahan kaduna na cewa, anfasa daura auren wata budurwa mai suna Yusra da angonta mai suna Auwal.
Biyo bayan sakamakon binciken lafiya da likita ya gabatar a zauren daura auren wanda ya nuna cewa amarya tana dauke da cutan HIV.
Kamar yadda kuka sani bisa al’ada kafin a daura aure ana kawo sakamakon binciken lafiya daga bangaren ango da amarya.
Domin gudun yaduwan cututtuka a cikin al’umma, saidai irin wannan binciken wani lokacin yakan bar baya da kura saboda ana samun rahotanni da yakesa a fasa yin aure daga sassa daban daban sakamakon irin wannan bincike.
Wata majiya ta bada rahoton fasa wani aure sakamakon bincike ya nuna amarya tana dauke da cutan kanjamau.
An shiga damuwa sosai sakamakon fasa wani aure a karaman hukuman kauru ta jahan kaduna, sakamakon fasa daura aure wani matashi.
Bayan waliyyan amarya da na ango sun hallara an kammala shigar da siga da komi da komi.
Bayan an kammala shigar da siga za’a daura auren saimai daurawan ya bukaci a gabatar da takarda shaidan gwajin lafiya na amarya dana ango.
Bayan da akace babu sai limamin yace, bazai daura auren ba saida takardan lafiya saboda haka ya bukaci ango da amarya suje suyi gwaji su kawo mishi takardan shaidan asibiti, inda nan da nan ango da amarya suka bazama asibiti akayi musu gwaji a mabanbantan asibiti.
Bayan wani lokaci sai ango da wakilanshi suka halarci wajen daurin auren dauke da takardunsu ta shaidan gwaji amma abun mamaki sai akaji waliyyan amarya shiru.
Nan akayi ta kai ruwa rana amma waliyyin amarya yace, mahaifiyan amarya taki basu shaidan lafiyan diyarta.
Hardai daga bisani aka gano ashe sakamakon gwaji yanuna amarya na dauke da cuta mai karya garkuwan jiki.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.