An Gano Sunayen Mutum Uku da Tinubu Ke Shirin Ba Manyan Mukamai a gwamantinsa.
Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, na kan gaba wajen maye gurbin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa
Wasu majiyoyi sun ce shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu, ya riga ya rubuta tawagarsa da zai kafa gwamnati da su
Haka nan an gano cewa Tinubu ya gama ynake tawagar tattalin arziki, inda aka hangi sunayen jiga-jigai a sahun gaba
Rahotanni da ke fitowa a halin yanzu sun nuna cewa zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, na shirin naɗa kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, a babban matsayin da zaran ya karɓi mulki.
Bayanan sun nuna cewa Tinubu na shirin gwangwale Gbajabiamila da muƙamin shugaban ma’aikatan fadarsa idan aka rantsar da shi ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, 2023.
Rahoton This Day ya ce, manyan mutane kamar Wale Edun, tsohon kwamishinan kuɗi a jihar Legas da kuma gwamnan jihar Kebbi mai ci, Atiku Bagudu, na cikin jerin sunayen da Tinubu ya ware wa babban muƙami.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa sunayen Mista Edun da Atiku Bagudu, sun fita a cikin tawagar ɓangaren tattalin arziki a gwamnatin Tinubu yayin da ake tunkarar rantsar da shi.
“Da yuwuwar Wale ne zai zama jagoran bangaren tattalin arziki, ko dai Ministan kuɗi ko kuma gwamnan babban bankin Najeriya (CBN). Har yanzun bamu da taƙamaiman shirin Tinubu kan Bagudu.”
“Amma yana cikin waɗanda da sunansu ya shiga ciki kuma zai ja ragamar babban ɓangare mai matuƙar muhimmanci a gwamnati mai kama wa.”
Idan zaku iya tunawa, Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Gbajabiamila na hanyar zama shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayyan Najeriya na gaba.
Wata majita ta daban da ta yi tsokaci kan wannan labarin, ta ce:
“Idan kuka tuna, bai karɓi shaidar cin zaɓe ba ranar Laraba, ba ya buƙatar Satifiket ɗin INEC, yana da duk abinda ya kamata an aiki a matsayin shugaban ma’aikatan shugaban kasa a sabuwar gwamnati.”
Rahoto Zuhair. Ali Ibrahim