An Gurfanar Da Matasa 5 Bisa Zargin Su Da Lakadawa Matar Aure Duka A Abuja.
An gurfanar da wasu matasa 5 a gaban wata kotu mai daraja ta ɗaya da ke Karu Abuja, bisa zarginsu da cin zarafin makwabcinsu da matarsa
Wadanda ake tuhuman Abuchi Njoku, Rejoice Njoku, Chidera Njoku, Nwanchukwu Chidera, da Mary Nwanchukwu, sun amsa laifin da suka aikata a lokacin da ‘yan sanda ke bincikarsu
Sai dai mutanen da ake tuhumar sun musanta zargin a gaban kotu wacce ta bayar da belinsu kan naira 100,000 kowannensu tare da kawo nagartaccen mutum guda daya ya tsaya musu
A ranar Larabar da ta gabata ne, rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da wasu matasa biyar a gaban wata kotu mai daraja ta ɗaya da ke Karu a Abuja, bisa zargin su da yi wa makwabcinsu da matarsa dukan tsiya.
Rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da Abuchi Njoku, Rejoice Njoku, Chidera Njoku, Nwanchukwu Chidera da Mary Nwanchukwu duka wadanda ke zaune a Jikwoyi Phase III, Abuja da laifin haɗa baki da ji wa magidantan rauni.
Lauyan masu shigar da kara, Mista Ade Adeyanju, ya shaidawa kotun cewa Anthony Okafor ne ya kai karar wadanda ake tuhuma, kan farmakin da suka kai masa shi da matarsa Ngozi.
Ya kara da cewa a yayin da ‘yan sanda ke bincikarsu, wadanda ake tuhumar sun amince da aikata laifin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Mai gabatar da kara ya ce Okafor ne ya kai rahoton lamarin, a ofishin ‘yan sanda na Jikwoyi da ke Abuja.
Ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 79 da na 240 na kundin laifuffuka na kasa.
Waɗanda ake tuhuma sun musanta zargin Sai dai wadanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin a gaban kotun.
Alkalin kotun, Malam Umar Mayina ya sanar da ba da belin wadanda ake tuhuma a kan kudi naira 100,000 kowannensu, tare da kuma kawo mutum daya da zai tsaya musu.
Alƙali ya dage sauraron ƙarar zuwa ranar 16 ga watan Yuni.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim