An gurfanar da wata mata gaban Kotu kan Naira dubu Uku a Enugu.
Wani mutum ya maka wata mata kotu saboda ta ki fitowa bayan ta karbi kudin sufurin N3k, ya umarce ta da ta biya N150k.
An kama wata mata bayan ta karɓi kuɗin mota dubu ukku N3,000 don ga ziyartar wanda yabata amma taƙi zuwa.
Mutumin ya kai ta kotu bisa cewa yabata kuɗi masu tarin yawa bisa zargin karya, kuma alkalin kotun ya umarce ta da ta biya shi N150k.
Mai shigar da ƙara ta shaida wa kotun cewa bayan ya aika mata da kudin ne ta kashe wayarta ta ki zuwa.
Wani lauya mai suna @egi_nupe ne ya raba shari’ar a shafin Twitter, wanda ya ce alƙalin kotun ya yanke wa matar diyya ne domin ya zama abin wa’azi gareta.
Labarin ya ce, “An bayar da rahoton cewa wata kotu a Enugu ta kafa misali mai kyau ta hanyar bayar da diyyar 150k ga wata matar, An ba ta 3k a matsayin kuɗin motar da yabata domin ta ziyarci wani saurayi, bayan ta karbo kuɗin sai ta kashe wayarta ta ki zuwa wurinsa.
“Abin da ya fusata da matakin da ya ɗauka, sai ya kawo rahoton tareda kai ƙarar ta bisa laifin yaudara.
A hukuncin da kotun ta yanke, alƙalin kotun ya ce matakin da matar ta ɗauka na yaudara ne kuma ya ba ta kuɗi har 150k domin ya zama tinkarar wasu masu irin wannan dabi’a na yaudara.”
RAHOTO:- Comrade Yusha’u Garba Shanga