An Halaka Ƙasurgumin Dan Bindiga A Kankara Jihar Katsina.
Rundunar Yan Sandan Jihar Katsina Ta Hallaka Dan Bindiga A Karamar Hukumar Kankara
Rundunar Yansandan Jihar Katsina ta samu nasarar hallaka wani da ake zargin Dan Bindiga ne a marabar Gurbi dake cikin karamar hukumar kankara.
Mai magana da yawun Rundunar Yansandan Jihar Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin Kwamishinan Yansandan Jihar.
Acewar sa, a ranar 14 ga watan yulin 2023, bayan samun bayanan sirri na cewar an ga yan bindiga a kauyen Marabar Gurbi, inda Baturen yansandan yankin ya isa wurin, domin Kai daukin gaggawa.
“Bayan ganin yansanda sun iso a inda suke, ya Sanya suka yi dauki ba dadi tsakanin yansandan da Yan bindigar. Bayan ruwan wuta da yansandan suka yi masu,r ya Sanya dole Yan bindigar suka fasa gudanar da mummunan aikin da suka shirya yi.” Inji ASP Abubakar.
Ya kara dacewar, bayan rugawar da yan bindigar su ka yi ne, yansanda suka duba wurin da akayi artabun, inda suka gano gawar wani daga cikin Yan bindigar.
ASP Abubakar Sadiq ya ce tuni Jami’an tsaron sun fara gagarumin Shiri na kamo sauran barayin dajin, bayan da take cigaba da bincike.