An Harbe Dalibin jami’ar Benin na shekarar karshe har lahira a dakin kwanan dalibai
A ranar Litinin din da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka bindige wani dalibin jami’ar Benin da aka fi sani da Desmond a shekarar karshe har lahira a dakinsa da ke dakin kwanan dalibai.
Marigayi dalibin da aka fi sani da ‘Maigida’ an ce yana cikin sashin kula da harkokin gwamnati kuma an harbe shi da misalin karfe 9 na daren ranar Litinin.
Lamarin ya haifar da firgici a tsakanin daliban. An kuma ce shi sarkin Kegite ne kafin a kashe shi.
Wani dalibin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce an harbe mamacin ne a fuska a inda babu ruwansa.
Dalibin ya ce, “Kisan Desmond ya haifar da firgici a makarantar. Dalibai ma suna tsoron zama a hostel. An harbe shi a fuska kuma ba shi da damar tsira daga harin.”
Ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, an tattaro cewa an ajiye gawarsa a dakin ajiyar gawa na asibitin koyarwa na jami’ar Benin.
Sai dai kuma yunkurin jin martani daga makarantar ya ci tura, domin ba a mayar da martani ga sakon WhatsApp da aka aika zuwa ga jami’ar hulda da jama’a na Jami’ar, Dr. Benedicta Ehanire ba.
Rahoto: Kamal Aliyu Sabongida