An Kai Samame A Masana’antar Jarirai A Abia.
Daga Al-Asad Al-Amin Funtua.
Masana’antun jarirai ta zama ruwan dare a Nijeriya, musamman a yankunan kudancin ‘kasar.
Sojoji sun kai samame a wata masana’antar jarirai da ke Umunkpeyi Nvosi, a karamar hukumar Isialangwa ta Kudu a jahar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na 14 Brigade, Ohafia, Laftanar Innocent Omale, ya fitar ya ce an kai samame ne bayan da aka samu labarin.
Kakakin rundunar ya bayyana sunan mamallakin masana’antar jarirai Nma Lilian Achumba, daga yankin Umunkpeyi, a karamar hukumar Isialangwa ta Kudu.
Ya bayyana cewa, an kubutar da ‘yan mata masu juna biyu 22, wanda akasarin su masu kananun shekaru ne daga masana’antar jarirai, an mika wadanda aka kubutar din ga gwamnatin jahar Abia.
Mai ba Gwamna Alex Otti shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Ferdinand Ekeoma ya yabawa rundunar Sojoji bisa farmakin da suka kai, inda ya bayyana cewa gwamnati ta himmatu wajen yaki da duk wani nau’in safarar yara da manya.