An Kama Matashi Dan Shekara 26 Da Ya Afakawa Yarinya Yar Shekara 7 A Bauchi.
Wani matashi dan shekaru 27 mai suna Ibrahim Abdullahi yana hannun ‘yan sanda a jahan Bauchi bisa zarginshi da aikataka lalata da wata yarinya ‘yar shekara 7 (wanda aka sakaya sunanta).
Wannan lamari ya farune a karaman hukuman Itas Gadau ta jahan Bauchi, bisani A cewan jami’an hulda da jama’a na rundunan ‘yan sandan (PPRO).
Mai kula da rundunan ‘yan sandan jahan Ahmed Mohammad Wakil yace, wanda ake zargin ya yaudari yarinya inda yashiga da ita bandaki dake makarantan firamare na Central Science dake garin Itas, daga bisani kuma yayi lalata da ita.
Kakakin rundunan ‘yan sandan SP ne ya ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa daya sanya ma hannu kuma ya baima manema labarai a Bauchi cewa, wani mai suna Umaru Yusuf ne yakai rahoton faruwan lamarin a hedikwatan ‘yan sandan Itas Gadau.
A cewan PPRO, da samun rahoton tawagan jami’an ‘yan sanda karkashin jagorancin DPO sun ziyarci inda lamarin ya faru, inda suka kai wadanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Itas Gadau yayinda aka kama wadanda ake zargin.
Lokacin da akeyi mishi tambayoyi wanda ake zargin ya amince da aikata laifin.
Ya kara da cewa ana cigaba da gudanar da bincike mai zurfi, bayan an kammala bincike za’a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin girban abinda ya shuka.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.