An kama wani mutum da ya bankawa dakin Bdurwansa wuta a Ogun.
A ranar 4 ga watan Afrilu ne wani mutum mai suna Yusuf Hassan mai shekaru 43, ya shiga hannun jami’an ‘yan sandan jihar Ogun da laifin kona gidan tsohuwar masoyiyansa Busayo Falola, lamarin da ya kai ga konewar ginin baki daya.
Da aka tambaye shi, da farko ya musanta cewa bai san komai ba game da lamarin, amma da DPO ya umurci jami’an tsaro da su je gidansa su gano ko yana gida a lokacin da lamarin ya faru, sai ya yanke shawarar ya bude baki ya furta cewa shi ne mutumin da ya aikata hakan.
Ya ci gaba da cewa ya yi niyyar kona tsohon masoyiyan nasa ne a gidanta saboda ya yi iya kokarinsa na sulhu da ita amma abin ya ci tura. Ya ce ya sayi man fetur Naira 500, ya zuba a dakinta ta taga ya banka masa wuta.