Rundunar ƴan sanda a jihar Katsina ta kama Maryam Habibu, ƴar shekara 18 da haihuwa, bisa zarginta da jefa ɗan kishiyarta mai shekaru hudu cikin rijiya a ƙaramar hukumar ƙafur ta jihar.
Maryam wadda ta fito daga ƙauyen Leko da ke ƙaramar hukumar Ɗanja tare da wasu mutane 11 da ake tuhuma da laifuka daban-daban da suka haɗa da fashi da makami da satar shanu, an gabatar dasu a ranar Juma’a a shelkwatar ƴan sanda da ke Katsina.
Kakakin rundunar ƴan sandan, SP Gambo Isah, yayin da yake zantawa da manema labarai yayin holan, ya bayyana cewa an kama matar ne a ranar 9 ga Nuwambar 2022. Ya ci gaba da bayyana cewar ta fitar da yaron ne ta jefa shi cikin rijiya. Kakakin ya ce Maryam da mahaifin yaron sun rabu.
Manema labarai sun rawaito cewa Maryam wadda ta zanta da manema labaran cikin harshen Hausa, ta amince da aikata laifin, tana mai cewa ƙaddara ce a wasa abun ya faru.
A cewarta, “Gaskiya ne na jefa yaron a cikin rijiyar da ya mutu amma Allah ne ya yi zai mutu a ranar. Shi ya sa ya rasu.”
A halin yanzu za’a cigaba da tsare matan a hannun Ƴan sanda har Lokacin da za’a gurfanar da ita a gaban kotu domin ta fuskanci hukunci.